Bayani kan Zamantakewar aure A Kasar Hausa

A zamantakewar aure, miji da mata suna da hakkoki da kowannensu ya kamata ya kiyaye. Abu na farko da ya kamata ma’aurata su sani shi ne: Allah ne Ya halicce su daga rai guda, wato annabi Adamu, sannan Ya halicci matarsa Hauwa’u daga gare shi domin samun natsuwa, to hakkin Allah a nan shi ne su bauta maSa Shi kadai ba tare da gwamutsa wani abu ba wajen bautar. Wannan ya hada da dukan sauran abubuwan da imani da Allah ya kunsa. Bayan wannan ya kamata ma’aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne shari’a ta dora wa kowannensu. Zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na mutu-ka-raba, domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga. Sanin hakkokin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure. Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci...